Jiya aka Gama Rana ta Hudu a Wasannin Olympics

Wasan Olympics

Rana ta hudu a gasar wasannin Olympics, wato jiya Talata, ta zo da cikas mafi muni a gasar ta lokacin sanyi na wannan shekarar.

Dan kasar Switzerland dinnan dan tseren bututun kankara "snowboarder" Louri Podladtchikov shi ya zo na daya a tseren rabin bututun maza, wanda hakan ya zama cikas ga wanda aka yi zaton shi sai yi na daya a karo na uku, wato ba-Amurke Shaun White, don ya ci lambar zinari.

'Yan kasar Japan Ayumu Hirano da Taku Hiraoka sun ci azurfa da tagulla, a yayin da kuma kasancewar White na hudu ya raba shi da bayyana a dakalin amsar lambobin yabon.

A harkokin na Olympic da ke wakana a Sochi, 'yar kasar Canada Dara Howell da 'yar kasar Jamus Carina Vogt sun yi abin tarihi. Howell ta ci zinari a gasar tseren kankara na mata, sannan kuma Vogt ita ta sami hakan a gasar tsalle ta mata.

Howell ta nuna murna sosai bayan nasararta, ta na mai cewa ta na alfaharin wakiltar kasar Canada.