Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Ta Aika Da Hujjojin Tsige Trump

Nancy Pelosi

Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi ta saka hannu kan takardun hujjojin tsige shugaban kasa Donald Trump da kuma aika tardun zuwa Majalisar Dokoki domin fara shari’a mako mai zuwa.

Pelosi ta yi amfani da alkaluma daban-daban wajen rubuta sunanta kan takardun, ta kuma mika su ga ‘yan Democrats shugabannin kwamitocin da suka yi aikin tsige shugaban kasar.

Manajojin tsige Trump, da ‘yan Majalisar da zasu gabatar da ‘kara, da akawun Majalisa, sune suka kai takardun hujjojin zuwa Majalisar Dattawa. Shugaban masu rinjaye a Majalisar Mitch McConnell ya ce yau Alhamis Majalisar za ta karbi takardun a hukumance.

A lokacin ne, za a rantsar da Alkalain Alkalan Amurka John Roberts wanda shine zai gudanar da shari’ar, daga nan kuma sai ya rantsar da Manajojin da Majalisar Wakilai ta aika.

Tun jiya Laraba ne, Majalisar Wakilan da ‘yan Democrats ke da rinjaye suka kada kuri’ar amincewa da manajojin da za a aika a zaman shari’ar. Cikinsu har da shugaban kwamitin tattara bayanan sirri Adam Schiff da shugaban kwamitin Shari’a Jerry Nadler.