KANO: Maniyyata Aikin Hajji Bana Na Zargin Hukumar Alhazai Da Rashin Cika Alkawari

Wasu Alhazai masu tafiyan aikin hajji

Alhazan jihar Kano da suka biya aikin hajjin bana ta hanyar asusun adashen gata suna zargin hukumar alhazai ta jihar da rashin cika alkawarin cewa sune rukunin farko da za’a baiwa fifiko a yayin raba kujerun aikin hajjin bana.

Sai dai hukumar alhazan ta Kano tace matsalar na da nasaba da kalubalen samo vizar alhazai daga hukumar aikin hajji ta kasa.

Galibin wadannan alhazai da suka biya kudaden su karkashin tsarin adashen gata da hukumar alhazan Najeriya ta bullo dashi, da nufin baiwa masu karamin karfi damar biyan kujerar hajji cikin sauki, sun biya kaso mai tsoka na kudaden nasu ne tun kusan shekaru biyu zuwa uku da suka shude.

Wasu maniyyata da ke tattauanawa a tsakanin su, sun nuna fusata a harabar hukumar alhazai ta Kano lokacin da suka je neman sanin makomar kujerun.

Maniyyatan dai sun koka kan yadda Jami’ai a hukumar ke musu jeka ka dawo. Sun ce dole ran su ya baci saboda an yaudare su bayan duk sun bi dokokin da aka fayyade musu.

Alhaji Abba Muhammad Danbatta dake zaman sakataren zartarwa na hukumar alhazan Kano ya yi tsokaci dangane da wannan batu. Ya ce shi dai ya na rokon hukumar alhazai ta Kano da ta taimaka ta samo ma wadannan alhazai biza da allocation da wuri.

Muryar Amurka ta kuma tuntubi kakakin hukumar kula da ayyukan hajji ta Najeriya Hajiya Fatima Sanda Usara, inda ta ce hukumar ta sami rahoto kan rashin samun kujeru ga alhazan da suka biya hajji bisa tsarin adashen gatan a jihar Kano, kuma za’a bincika domin daukar matakan warware matsalar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti :

Your browser doesn’t support HTML5

KANO: Alhazan Hajji Bana Na Zargin Hukumar Alhazai Da Rashin Cika Alkawari