‘Kara Yawan Jami’an Tsaro Shine Zai Tabbatar Da Zaman Lafiya a Najeriya

Wani mutum na wucewa ta kusa da motar 'yan sanda

Masana harkokin tsaro a Najeriya na ganin ‘karin daukar jami’an ‘Yan Sanda aiki shine masalahar tsaro a kasar.

Ba sabon abu bane batun bindigogi ko makaman dake hannun bata gari sun fi na jami’an tsaron Najeriya inganci, amma bangaren kwarewar aiki ko iya sarrafa makaman fa?

Jami’in ‘Yan Sanda mai ritaya CSP Ibrahim Gabanni, ya ce ‘Yan Sandan Najeriya za su iya rawar gani a ko ina a fadin duniya, musammamma idan aka cusa musu kishin ‘kasa.

Shi kuma mai sharhi kan lamuran tsaro Babangida Turaki, na ganin na ganin idan har aka ‘kara daukar jami’an ‘Yan Sanda shine masalahar tsaro a Najeriya. Ganin yadda yawan jama’ar dake a kasar, kuma ‘Yan Sandan dake kula da al’ummar basu kai yawan da ya kamata ba.

Sai dai kuma malaman addini na ganin dagewa da addu’a shine zai saka zaman lafiyan da ake samu a yanzu ya ci gaba da daurewa.

Domin karin bayani saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

‘Kara Yawan Jami’an Tsaro Shine Zai Tabbatar Da Zaman Lafiya a Najeriya - 2'41"