Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Bauchi Ya Zabi Sabon Mataimaki


Gwamnan JIhar Bauchi Barrister Muhammed Abdullahi Abubakar
Gwamnan JIhar Bauchi Barrister Muhammed Abdullahi Abubakar

Kasa da makwanni biyu bayan da mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Alhaji Nuhu Gidado ya yi murabus daga mukaminsa, gwamnan jihar Muhammad ABubakar, ya zabi sabon mataimaki.

Gwamnan jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, Muhammad Abubakar, ya zabi shugaban ma’aikatan fadar gwamtinsa, Alhaji Audu Sule Katagum a matsayin sabon mataimakinsa.

Kwamishinan yada labaran jiyar, Alhaji Umar Sade ne ya bayyana hakan a jiya Asabar, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito a shafinta na yanar gizo.

“Gwamnan ya zabi Audu Sule Katagum a matsayin mataimakin gwamna, bayan tuntubar masu ruwa da tsaki a jihar.” Inji Kwamishinan.

Yanzu haka, jami’in yada labarai a majalisar dokokin jihar ta Bauchi Mr. Lamara Chinade, ya ce an gabatar da sunan Katagum a gaban majalsiar.

Ya ce mai yiwuwa a gayyaci shi a zauren majalisar a mako mai zuwa domin a tantance shi.

Kusan makwanni biyu da suka gabata ne mataimakin gwamnan jihar ta Bauchi, Alhaji Nuhu Gidado, ya yi murabus daga mukaminsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG