Kasashen Gabar Teku Sunyi Atisaye Domin Shawo Kan Matsalar Ta'adandanci

Vice Admiral IE Ibas - Chief of Naval Staff

Rundunar sojojin ruwa ta kasar Faransa ta fara jagorantar wani atisayen kwanaki 5 na mayakan ruwan kasashen gabar tekun Guinea. Atisayen wanda ya kunshi manyan jiragen yaki, da jiragen sama masu saukar ungulu na sojojin, don karfafa tsaro ta cikin ruwa.

Kakakin hedkwatar rundunar sojojin ruwan Najeriya Navy Commodore Sulyman Dahun ya shaidawa Muryar Amurka cewa atisayen, bayan kara nagartar aikin mayakan, zai kuma taimaka wajen karfafa hadin guiwa.

Commodore Sulyman Dahun yayi bayanin cewa ba wata kasa da zata iya tunkarar .matsalolin tsaro a gabar tekun Guinea, ba tare da hadinkai ba

A Karshen wannan atisaye ana sa ran zai taimakawa dakarun ruwan kasashen wajen shawo kan kalubalen tsaro a tekun.

Ga rahoto cikin sauti daga wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Kasashen Gabar Teku Sunyi Atisayen Domin Shawo Kan Matsalar Ta'adandanci