Kashi 60 Zuwa 80 Na ‘Yan Kallo Za A Bari Su Shiga Kallon Wasannin Gasar AFCON Saboda COVID - CAF

Daya daga cikin filayen da za a buga gasar AFCON a Kamaru (Facebook/CAF)

A tsakanin watannin Yuni da Yulin bara ya kamata a yi gasar, amma annobar COVID ta sa aka dage zuwa bana.

Hukumar Kwallon Kafa ta nahiyar Afirka CAF ta ce kashi 60 zuwa 80 na ‘yan kallo za a bari su shiga filayen wasanni da za a kara gasar cin kofin nahiyar na AFCON.

Matakin a cewar hukumar na da nasaba da annobar COVID-19.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, CAF ta ce bayan wata tattaunawa da ta yi da hukumomin cikin gida na Kamaru, sun cimma matsaya akan cewa kowanne filin wasa za a bar ‘yan kallo kashi 60 ne zuwa 80 su shiga kallo.

A ranar 9 ga watan nan na Janairu za a bude gasar ta cin kofin nahiyar Afirka, wacce Kamaru ke karbar bakunci.

Za kuma a kammala a ranar 6 ga watan Fabrairu kamar yadda jadawali gasar ya nuna.

A tsakanin watannin Yuni da Yulin bara ya kamata a yi gasar, amma annobar COVID ta sa aka dage zuwa bana.

Kasar Aljeriya ce ke rike da kofin gasar.