Kawunan 'Yan Yobe Sun Rabu Akan Zaben Gwamna

Alhaji Ibrahim Geidam, gwamnan jihar Yobe.

Dai dai lokacin da ake tababan yin zabe a jihohin dake karkashin dokar ta baci sabili da rigingimun Boko Haram sai gashi an samu rabuwar kawunan 'yan Yobe akan zaben gwamna idan har za'a yi zaben.

Yanzu dai babu tabas cewa za'a gudanar da zabe a jihohin dake karkashin dokar ta baci domin wasu sassan jihohin Borno da Adamawa suna hannun 'yan Boko Haram inda suka yi ikirarin kafa tasu daular sarda nada sarakuna.

Sai dai a jihar Yobe wasu 'yan jihar suna neman canza akalar kujerar gwamnan jihar zuwa nasu shiyar domin su ma su samu damar dana kujerar gwamnan jihar kamar sauran sassan na jihar.

Wasu kungiyoyi a jihar sun yi taron inda suka kira gwamnan na yanzu ya zarce bisa ga la'akari da ayyukan da suka ce gwamnan yayi masu. To amma 'yan jam'iyyar APC jam'iyyar dake mulki a jihar suna ganin akwai bukatar sake shiri domin suna ganin ya kamata duk shiyoyin jihar su sama damar hawa kujerar gwamnan.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

Your browser doesn’t support HTML5

Kawunan 'Yan Taraba Sun Rabu Akan Zaben Gwamna - 3' 10"

Karin Bayani akan Rahoto na Musamman a Kan Boko Haram: Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi >>