Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Najeriya Ta Ce Mohammed Bashir, Wanda Ke Amfani Da Sunan Abubakar Shekau, Ya Mutu, 25 Satumba, 2014

Gwamnatin Najeriya ta ce al'ummar yankin dake fama da rikicin Boko Haram sun tabbatar da bayanan da aka samu a game da usulin Bashir Mohammed mai amfani da sunayen da suka hada da Abubakar Shekau, Abacha Abdullahi Geidam, Damasak, da wasunsu. An kashe Bashir a wani fadan da aka gwabza kwanakin baya a kusa da Maiduguri. Haka kuma, rundunar sojojin Najeriya ta ce wasu mayakan Boko Haram su 135 sun mika kawunansu da makamansu ga hukumomi a yankin karamar hukumar Biu, dake Jihar Borno. Guda 88 sun yi saranda a Mairiga/Buni-Yadi, wasu 45 kuma a tsakanin Mubi da Michika.

Domin Kari

XS
SM
MD
LG