Korafi Game Da Zirga-zirgar Jiragen Sama A Nijeriya

  • Ibrahim Garba

Wani jirgin sama na shirin sauka a filin jirgin saman Kasa da kasa na Murtala da ke Lagos, Nijeriya.

Wani Kwararra a harkar zirga-zirgar jiragen sama kuma tsohon Sakatare-Janar na kungiyar masu harhar zirga-zirgar jiragen sama a Nijeriya mai suna keftin Muhammad Joji, ya ce ba a yi wa arewa adalci ba a kason zirga-zirgar jiragen sama a kasar.
Tsohon Sakatare Janar na Kungiyar masu harkar jirgin sama a Nijeriya, Keftin Muhammad Joji ya ce matakan da ake daukawa na baya bayan nan a Ma’aikatar Zirga-zirgar jiragen saman Nijeriya na durkusar da harkar jiragen sama a arewacin Nijeriya. A hirar su da Ibrahim Alfa Ahmed, Keftin Joji ya yi misali da yadda aka bai wa kamfanin jirgin saman Habasha umurnin ya bar arewa ya rinka tashi a filin jirgin saman Enugu. Ya kuma ce hatta kamfanin jirgin saman Qatar ana so a rage harkokinsa a arewacin
Nijeriya.

Ya ce tun a shekara ta 2008 aka bai wa kamfanin jrgin saman Qatar izinin zirga –zirga a Lagos da Kano har sau bakwai-bakwai amma ba su fara na Kano nan da nan ba. Ya ce hatta ran 2 ga watan shida na wannan shekarar an tafi birnin Doha, inda aka sake tabbatar da cewa ba a canza yarjajjeniyar ta 2008 ba.

Game da matsayin Kano a harkar jirgin sama kuma, Keftin Joji y ace tun a 1925 jirgi ya fara sauka a Nijeriya a filin jirgin saman Kano. Daga 1955 zuwa 1956 jiragen sama wajen 377 ne kan tashi daga filin jirgin saman Kano zuwa kasashen waje saboda a lokacin Kano ne cibiyar harkokin jiragen sama. Ya ce ko gyarar da aka ce an yi shekarun baya don sabunta fiilin jirgin saman Kano zance ne kawai saboda har yanzu ba a iya abin da aka ce za a yi na jigilar jama’a da kaya idan an sabunta filin jirgin saman saboda rashin inganci. An fi fifita filayen jirgin saman kudanci in ji shi.

Your browser doesn’t support HTML5

Korafi Game da Zirga Zirgar Jirage a Nijeriya - 3:39