Accessibility links

Mutane 14 Suka Mutu A Hadarin Jirgin Associated Airlines

  • Grace Alheri Abdu

Wani dan sanda a kusa da inda jirgi ya fadi

Ministar harkokin sufurin jiragen sama ta Najeriya Stella Uduah ta tabbatar da mutuwar mutane 14 a hadarin jirgin saman Associated Airlines mai lamba SCD 361.

Ministar harkokin sufurin jiragen sama ta Najeriya Stella Uduah ta tabbatar da mutuwar mutane 14 a hadarin jirgin saman Associated Airlines mai lamba SCD 361. Ministar ta bayyana cewa, jami’an aikin ceton gaggawa da ma’aikatar kashe gobara da kuma jami’an tsaro sun isa wurin nan da nan inda suka iya gano wadansu gagarwaki yayinda aka dauki wadanda suka ji raunuka zuwa asibiti.

Jirgin ya game da hatsari ne yana kokarin tashi a tashar jirgin sama ta Murtala dake birnin Ikko da misalin karfe tara da rabi na safe dauke da fasinjoji da ma’aikata 20.
Fasinjojin dake cikin jirgin sun hada da: Feyi Agagu, Femi Akinsanya, Akintunde Joseph, Akeem Akintunde, Tunji Okusanya, Chijioke Duru, Kingsley Amaechi, Deji Afolabi, Mrs. E.O. Alabi, Daji Bernard, Deji Falae, Samson Hassan da kuma Olatunji Okusanya.

Akwai kuma ma’aikatan jirgi guda bakwai da suka hada da : Capt. Yakubu, Oyinlola, Engr. Saroh Elaiye, Ibrahim, Mr. Felix Tatoye, Owolabi, Samson.

Wakilin Sashen Hausa Ladan Ibrahim Ayawa yaje tashar jirgin saman inda ya dauko mana karin bayani.

XS
SM
MD
LG