Kotu Tayi Hukunci Akan Karar da Lamido Sanusi Ya Shigar

Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi.

Biyo bayan yadda gwamnatin tarayya ta tsige Sanusi lamido Sanusi sai ya ruga kotu neman hakinsa kotu kuma ta bashi duk abubuwan da ya bukata
Karar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi ya shigar , kotu ta yanke hukunci.

Mai shari'a Ibrahim Uba ya yanke hukunci kan karar da Sanusi Lamido Sanusi ya shigar dangane da yadda gwamnatin tarayya ta cireshi daga mukaminsa. Mai shari'a yace a bisa ga tsarin Najeriya gwamnati bata yiwa tsohon gwamnan daidai ba, a takaice ta ci zarafinsa ta kuma taka masa hakinsa. Sabili da haka Alkali Ibrahim Uba ya umurci gwamnatin tarayya ta biya Malam Sanusi Lamido Sanusi nera miliyan hamsin kana ya sake ba gwamnatin tarayya da 'yansanda masu sa farin kaya wato SSS umurni su gaggauta su mayarwa Sanusi takardar fasfo dinshi. Bugu da kari alkalin ya umurci gwamnatin tarayya ta rubuta takardar ta musamman na bashi hakuri domin an keta masa haddi a matsayinsa na dan kasa.

Victoria Alonge lauyar tsohon gwamnan tace kamar yadda manema labarai suka ji duk abubuwan da suka nema mai shari'a ya basu kama daga cewa a biya Sanusi nera miliyan hamsin zuwa ga batun fasfo nashi da kuma uwa uba takardar bada hakuri da aka ce gwamnatin tarayya ta rubuta masa.

Tace a dokar kasar Najeriya ba za'a tsare mutum ba ba tare da bayar da dalilin yin hakan ba. An tsareshi na sa'o'i kuma ba'a gaya masa dalilin yi masa hakan ba.

To saidai da aka tuntubi lauyan gwamnatin tarayya sai yace shi ba zai ce komi ba, ba tare da izinin gwamnati ba. Amma yace ko shakka babu gwamnati zata daukaka kara.

Da ma can Sanusi Lamido Sanusi yace gwamnatin tarayya bata da hurumi ko ikon cireshi daga mukaminsa dalili ke nan da yace zai kai gwamnati kara ba domin kansa ba a'a domin masu zuwa nan gaba da kuma kare mutuncin bankin domin kada a mayarda shi wani bangare na ofishin shugaban kasa.

Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.

Your browser doesn’t support HTML5

Kotu ta Yanke Hukunci kan Karar da Lamido Sanusi Ya Kai Gwamnatin Tarayya - 2'10"