Accessibility links

Kyakyawan Yanayin Kasuwanci Shi ke Inganta Harkokin Kasuwanci a Duniya


Kofar wata masana'anta dake rufe.

Kyakyawan Yanayin Kasuwancin ne 'yan kasuwar Najeriya ke bukata domin tafiyar da harkokin Kasuwanci yadda ya kamata.

Mataimakin shugaban 'yan kasuwa da masana'antu da aikin gona na Najeriya, kuma shugaban wannan kungiya na shiyyar arewa, Sanusi Mai Jama'a Ajiya ne ya bayana haka a wata tattaunawar da yayi da Muryar Amurka a birnin Washington.

Sanusi Ajiya yace kasashen duniya da suka ci gaba na tattare da shuwagabani masu aiki tukuru domin ganin 'yan kasuwa sun sami kyakyawan yanayi domin bunkasar kasuwanci.

A cewarshi, babu ruwan gwamnati da kasuwanci, amma dokokin da take yi akan harkokin kasuwanci wajibi ne ta ringa tuntubar 'yan kasuwa domin samun ra'ayoyinsu dangane da haka.

A wani labari kuma tsohon dan majalisar wakilai,mai wakiltar mazabar Katagum ya gwamnati,sai dai ta taimaka da bukatun 'yan kasuwa da yakamata akan harkokin kasuwa domin kasuwanci ya tsaya dai-dai.

Ya kara da cewa dogaro da gwamnati bana dan kasuwa bane.


XS
SM
MD
LG