Kotun ICC Ta Tabbatar Da Hukuncin Daurin Shekaru 25 Ga Dominic Ongwen

Dominic Ongwen A Kotun ICC

Ongwen, mai shekaru 40 a yanzu, an sace shi yana dan shekara 9 kuma aka tilasta masa shiga cikin rayuwar tashin hankali bayan da kungiayr da ta sace shi din ta kashe iyayensa.

Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa a ranar Alhamis ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 25 da aka yanke wa Dominic Ongwen, wani tsohon soja da ya shiga aikin soja yana karamin yaro a kasar Uganda, wanda ya zama kwamanda a kungiyar ‘yan tawaye ta Lord Resistance Army, kuma ya amince da hukunci daurin shekaru 25 da aka yanke masa na fyade, kisa da kuma sace yara.

Mai shari’ar da ta jagoranci alkalan kotun, Luz del Carmen Ibanez Carranza ta ce, “Kotun daukaka karar ta yi watsi da duk wasu dalilai na kariya na daukaka kara kuma gaba dayansu sun tabbatar da hukuncin.”

Alkalan Kotun ICC Da Ke Hague

Daga baya alkalan sun kuma yi watsi da dukkan dalilan daukaka karar da suka shafi hukuncin.

Kwamandan yakin da ake nema ruwa a jallo, Joseph Kony, ya jagoranci kungiyar LRA da ta addabi 'yan kasar Uganda na kusan tsawon shekaru 20 a lokacin da ta ke yakar gwamnatin shugaba Yoweri Museveni daga sansanoni a arewacin Uganda da kuma kasashe makwabta.

An dai yi nasarar kawar da mayakan da dama.

Ongwen, mai shekaru 40 a yanzu, an sace shi yana dan shekara 9, kuma aka tilasta masa shiga cikin rayuwar tashin hankali, bayan da kungiayr ta kashe iyayensa.