Kungiyar Izala a Najeriya Ta Kaddamar Da Kwalejin Kiwon Lafiya Ta Musulunci Ta Farko A Ghana

TARO A GHANA

A karon farko an bude katafaren kwalejin koyar da nassoshi na ta Musulunci a Ghana.

Taron da mataimakin shugaban Ghana Dakta Mahmud Bawumia ya jagoranta ya samu halartar manyan shugabannin kungiyar Izala na Ghana tare da tarayyar Najeriya, ciki harda Sheikh Abdulai Bala Lau da Sheikh Kabiru Gombe da dai sauransu.

TARO

Yayin jawabinsa mataimakin shugaban kasar Ghana, Dakta Mahmud Bawumia ya ce Ghana nada kwalejojin koyar da nassoshi fiye da 90 amma saboda shirin daukar dawainiyar karatun dalibai ta FREE SHS da gwamnatinsa ta inganta ya sa kwalejojin ba su iya daukar daliban da suka kammala sakandare ba.

KWALEJIN NESOSI

A don haka wannan sabuwar kwalejin ta Musulunci za ta taimaka sosai gurin bunkasa cigaban harkar lafiya a kasar.

Shi kuwa Shugaban Jibwis a Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce wannan makarantar da aka bude na bukatar taimako gurin gwamnati kamar yadda 'yan izala na Ghana da Najeriya su ka bada gudunmuwa gurin gina ta domin irin wannan ilimi ya bunkasa a fadin kasar Ghana.