Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar United Krorbo Ta Kalubalanci Shirin Maido Da Mayakan Gargajiya a Ghana


NENE SAKITE II (modernghana.com)
NENE SAKITE II (modernghana.com)

A Ghana, kungiyar masu matsa lamba ta siyasa, United Krobo Foundation, ta ce tana adawa da shirin majalisar gargajiya a yankin na sake dawo da mayaka na gargajiya a cikin al'umma.

Ta ce shirin zai gurgunta ayyukan ‘yan sanda wadanda shugabannin kungiyar suka ce an ba su damar tabbatar da doka da oda.

Mai magana da yawun Majalisar Gargajiya ta Manya Krobo, Nene Asada Ahor ta shaidawa wakilin Muryar Amurka na Sashen Ingilishi cewa, gidauniyar United Krobo, kungiya ce da ba a amince da ita ba.

A cewar Kakakin, ayyukan kungiyar na haifar da tashin hankali da rashin jituwa a yankin.

Wannan na zuwa ne bayan Nene Sakite na biyu, shugaban yankin gargajiya na Manya Krobo a yankin Gabashin Ghana, ya sanar da cewa majalisar gargajiya ta yanke shawarar dawo da amfani da mayaka na gargajiya.

Matakin, a cewar shugaban, zai taimaka wajen yaki da rashin da'a a yankin. Kafofin yada labarai na cikin gida sun ba da rahoton tashin hankali tsakanin majalisar gargajiya da mambobin gidauniyar United Krobo.

Hakan ya biyo bayan zanga-zangar da kungiyar ta shirya wanda ‘yan sanda suka amince da su amma ba tare da sun nemi izini daga majalisar gargajiya ba.

Shugabannin gidauniyar United Krobo sun ce da alama dawo da mayaka na gargajiya hanya ce da majalisar gargajiya za ta dakile ayyukansu.

Ita dai kungiyar ta United Krobo Foundation ta kasance jagora a fafutuka da gudanar da zanga zangar adawa kan yadda ake raba wutar lantarki a yankin da yadda suke biyan makudan kudaden wutar kamar yadda jaridar Ghana web ta wallafa.

XS
SM
MD
LG