Tarayyar kasashen Afrika ta yi lale da dawowar kasar Morocco cikin kungiyar kasashen bayan fiye da shekaru 30 da kasar ta kwashe bata cikin tarayyar.
WASHINGTON, DC —
Duk da dai ba lallai bane dawowar kasar komai ya tafi daidai, shugabannin afirka sun ce hadin kan afrika ya fi muhimmanci a a wanna zamanin na canji da ake ciki a duniya.
A shekarar aluf dari tara da tamanin da 4 ne kasar morocco ta fita daga tarayyar saboda tarayyar Afrika ta yarda da samun ‘yancin yammacin yankin Sahara da aka yi ta takaddama akai.
Shugabannin Afrika sun ce a karshe, shawarar barin morocco ta dawo zabi ne na hadin kai da yarjejeniya.