Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Morocco Ta Koma Kungiyar Hadin Kan Kasashen Afirka AU


Shugabannin kasashen Afirka a taronsu na AU a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha ko Ethiopia

Taron da suka soma jiya Litinin ya samu kasancewar kasar Morocco a karon farko bayan fiye da shekaru talatin da ta fice daga kungiyar saboda mallakar yakin Sahara da tayi da kungiyar bata amince mata ba kuma a wannan karon ma bata canza zani ba.

Inji masu sharhi kungiyar AU ta hadin kan kasashen Afirka, kungiya ce da yakamata ta hada kawunan kasashen a zahiri.

Kamata yayi tayi duk iyakacin kokarinta ta tabbatar da mulkin dimokradiya a duk fadin nahiyar da tabbatar da kwanciyar hankali da taimakawa kasashen su farfado da tattalin arzikinsu ta yin cudanya da juna.

Kasar Morocco da yanzu ta dawo cikin kungiyar tana da karfi a harkokin kasuwanci da siyasa da kuma taimakawa kasashe a harkokin tsaro. Zamansu a ware kamar yadda Morocco tayi ba abun da zai gyara kasashen Afirka ba ne. Saboda mahimmancinta ya sa da zara ta furta aniyyar komowa suka yi maza-maza suka karbeta.

Dangane da cewa matsalar da ta sa Morocco ta fice da can, wato batun yankin Yammacin Sahara masu sharhi na ganin yakamata a wuce wannan maganar yanzu, wadda tamkar karamar matsala ce.

Abun da shugabannin suka sa gaba shi ne abun da zasu iya kullawa talakawansu domin a samu cigaba.

Shugaban Guinea Conakry shi ne zai shugabanci kungiyar yanzu kuma ana ganin rawar da ya taka wurin warware rikicin Gambia ya sa aka amince masa. Hazakar da ya nuna cewa yana iya shiga gaba ya sa aka bashi shugabancin kungiyar.

Shi ma ministan harkokin wajen Chadi Muhammad Musa ya samu shugabancin hukumar kungiyar sanadiyar rawar da kasarsa ta taka a

harkokin tsaro, wato yaki da Boko Haram a yankin kasashen Sahel.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye


Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG