Lauyan maharin birnin Faris na son a maida shi Faransa

Lokacin Da Aka Damke Salah Abdelslam a Belgium

Babban mai gabatar da kara na kasar Faransa yace, jigon da ake zargin da kitsa mummunan harin da aka kai a Paris har mutane 130 suka mutu yace, yaso tada kansa da Bam a Stadiyam din kwallo amma ya fasa.

An sallami Salah Abdeslam daga asibitin da ‘yan sanda suka kaisi sakamakon raunin da ya samu a kafa da ake kokarin kama shi a samamen da aka kai a unguwar Molenbeek dake Brussels ta kasar Belgium.

An kuma wuce da shi zuwa gidan yari tare da wani da aka kama su tare a samamen. Lauyan Salah din wato Sven Mary, yace Abdeslam na bawa ‘yan sandan Belgium hadin kai, don haka zai nemi shari’a ta mayar shi kasar Faransa.

Mai gabatar da kara na Faransa Francios Molins yace, ya kamata a dauki wannan magana ta Salah da muhimmanci game da cewa da yaso tada kansa a filin kwallon kafa amma ya fasa.