Lewandowski Ya Taimakawa Barcelona Ta Tsallake Rijiya Da Baya

Lewandoski

Yanzu Barcelona na matsayi na uku a teburin rukunin C da maki hudu, wato Inter ta sha gabanta da maki uku, a kokarin da kowannensu ke yi na samun matsayi na biyu a rukunin a gasar ta UEFA.

Robert Lewandowski ya zura kwallon da ta taimakawa Barcelona wajen ci gaba da zama a gasar Zakarun Nahiyar Turai ta UEFA a ranar Laraba.

Kwallon Lewandowski da ya ci da ka, ita tallafawa zakarun na Catalan aka tashi da ci 3-3.

Gabanin hakan wasan na 3-2 inda Inter take gaba bayan da dan wasanta Robin Gosens ya zura kwallonsa a minti na 89.

Da a ce Barcelona ta sha kaye a wannan wasa, da ta fice kenan daga gasar a matakin rukunin na Champions a karo na biyu a jere.

Amma duk da haka, har yanzu yaran na Xavi Hernandez na bakin kura, saboda Barcelona yanzu na matsayi na uku a teburin rukunin da maki hudu, wato Inter ta sha gabanta da maki uku, a kokarin da kowannensu ke yi na samun matsayi na biyu a rukunin na C.

Bayern Munich wacce ta doke Viktoria Plzen da ci 4-2 a nasararta ta hudu a jere, na da maki 12.

Yanzu Inter za ta gamu da Plzen a Italiya sannan ta hadu da Bayern a wasan gaba, yayin da Barcelona kuma za ta hadu da Bayern da farko sannan ta kara Plzen daga baya.