Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasannin UEFA Da Za A Buga A Wannan Mako


'Yan wasan Chelsea da za su kara da Lille na kasar Faransa
'Yan wasan Chelsea da za su kara da Lille na kasar Faransa

Wani babban wasa da masu sha’awar kwallon kafa suka kasa suka tsare shi ne wasan Atletico Madrid da Manchester United inda ‘yan wasan kasar Uruguay Luis Suarez da Edison Cavani za su hadu.

A wannan mako ne za a shiga rukunin wasanni na biyu na ‘yan 16 a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai ta UEFA Champions League.

A ranar Talata Chelsea mai rike da kofin gasar za ta karbi bakuncin Lille ta kasar Faransa inda ‘yan wasa irinsu Romelu Lukaku na Chelsea da Jonathan David na Lille za su nuna kwarewarsu.

Kazalika a ranar ta Talata Juventus ta kasar Italiya za ta kai wa Villareal ta kasar Spain ziyara.

Wani babban wasa da masu sha’awar kwallon kafa suka kasa suka tsare shi ne wasan Atletico Madrid da Manchester United inda ‘yan wasan kasar Uruguay biyu za su kara, wato Luis Suarez na Atletico da kuma Edison Cavani na Manchester United.

Za a buga wasan ne a ranar Laraba, inda Atletico za ta karbi bakuncin United.

Wasa na biyu a ranar Laraba shi ne karawa tsakanin Benfica da Ajax.

Benfica na tunkaho da zakakuran ‘yan wasa yayin da Ajax wacce tauraronta ke haskawa a ciki da wajen gida take shirin ziyartar ta.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG