Ma'aikata A Jihar Kano Sun Koka Akan Zaftare Musu Albashi

Yayin da al'ummar Musulmin duniya ke shirye-shiryen bukukuwan karamar sallah bayan kammala Ibadar Azumin Ramadan a cikin alhinin annobar coronavirus, ma’aikata a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya sun yi korafi akan yadda gwamnatin jihar ta zaftare musu albashin watan nan na Mayu.

Comrade Kabiru Ado Minjibir, da ke zaman shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya reshen jihar Kano, ya bayyana damuwa game da wannan mataki, ya ce gwamnati ba ta tuntube su game da lamarin ba kafin ta zartar da hakan.

Ya kara da cewa kungiyar kwadagon jihar Kano, ba ta da wata masaniya akan wannan batu, kuma a ka'idance bai kamata a taba albashin ma'ikata ba, sai an sanar da wakilansu, tunda albashi kusan wata yarjejeniya ce a rubuce.

To amma kwamishinan kudi na jihar Kano Alhaji Shehu Na-Allah, ya bayyana cewa kudin da gwamnatin Najeriya ta raba wa jihohi, sai ya kasance ba za su isa biyan albashi ba a jihar Kano saboda jihar na biyan ma'aikatanta sabon tsarin albashi na naira 30,600.

Ya kuma ce saboda tausayi da kulawar da gwamnati ke yi wa al'umma da ma'aikatan jihar, kuma duba da cewa watan Ramadan ya zo karshe ya sa gwamnati daukar matakin yin amfani da tsarin albashin baya.

Saurari karin bayani cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Ma'aikata A Jihar Kano Sun Koka Akan Zaftare Musu Albashi