Mahukuntan Jihar Kaduna Sun Musunta Batun Rarraba Masarautar Zazzau

Gwamnan Kaduna Malam Nasiru El Rufa'i.

Jinkiri da mahukunta suke yi wurin nadin sabon sarkin Zazzau na ci gaba da jawo cece-kuce da kuma yada labarai mabanbanta game da masarautar, ciki har da maganar rarraba masarautar zuwa gida uku.

Tun yammacin ranar Lahadin da aka sa za a bayyana sunan sabon sarkin Zazzau ne dai wasu su ka fara yada labarin cewa gwamnati na niyar raba masarautar yi shi yasa har yanzu ba a nada sabon sarkin Zazzau ba.

Bayanin gwamnan jahar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-rufa'i a wajen gabatar da kasafin kudi na badi gaban majalisa, ya kara karfafa jita-jitar raba masarautar saboda kudurin da gwamnan ya ce zai kawowa 'yan majalisa don yin kwaskwarima ga masarautun jahar Kaduna. Sai dai kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya musanta wannan rade-radi.

Ya kwatanta labaran da ake yadawa da na kanzon kurege, saboda ya ce babu wani kudurin doka da hukumar zartarwa ta gabatar wa majalisar dokokin jiha dake neman kacaccala masarautar Zazzau. Ya kuma yi kira da jama’a su kwantar da hankalin su, nan bada dadewa ba za a bayyana suna sabon sarkin Zazzau.

Ita ma dai majalisar dokokin jihar Kaduna ta ce babu wani kudurin doka game da raba masarautar Zazzau kamar yadda Dan-majalisar mai wakiltar Zaria a majalisar Sulaiman Ibrahim Dabo, wanda shima mai sarauta ne na wakilin Birni Zazzau ya tabbatar a shafinsa na sada zumunta ya kuma tabbatarwa da Muryar Amurka cewa, babu wani kudirin doka irin haka.

Bisa ga cewar Fagacin Zazzau Alh Ibrahim Abubakar Yahaya, Masarautar Zazzau ta karyata wannan batun da ake ta yadawa

Al’umar Zazzau da dama dai sun sa ran jin sunan sabon sarki a ranar Lahadin da ta gabata wato kwanaki goma sha hudu da rasuwar mai martaba Sarkin Zazzau Alh Shehu Idris.

Tuni dai zaman zullumi da kuma sa ran jin sunan sabon sarkin Zazzau ya sanya jibge jami'an tsaro a bakin fadar sarkin Zazzau don gudun abin da ka iya tasowa.

Ga dai rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna a Najeriya:

Your browser doesn’t support HTML5

Mahukuntan Jihar Kaduna Sun Musunta Batun Rarraba Masarautar Zazzau-4:00"