Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sunayen Masu Neman Sarautar Zazzau Ba Su Zo Hannuna Ba – El-Rufai


Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El Rufai (Hoto: Shafin Twitter @elrufai)
Gwamnan Jihar Kaduna Nasiru El Rufai (Hoto: Shafin Twitter @elrufai)

Gwamnan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, Malam Nasiru El-Rufai ya ce sunayen masu neman kujerar masarautar Zazzau ba su kai ga hannunsa ba.

A ranar Juma’a rahotanni da dama sun nuna cewa masarautar ta Zazzau ta aika wa da gwamnan sunan mutum uku domin ya zabi mutum daya daga cikinsu.

Amma a shafinsa na Twitter El-Rufai ya bayyana akasin hakan.

“A KIYAYE LABARIN KANZON KUREGE! @elrufai bai karbi komai ba. Kwamishinan da ke kula da harkokin masarautu yana duba sunayen mutum 11 da ke takarar neman kujerar tare da yin nazarin abubuwan da masu zaben sarki suka bayyana akansu.”

Gwamnan na Kaduna ya kara da cewa, “zan duba shawarwarin da aka bayar sannan na zabi Sarki na gaba IN Sha Allah.”

A dai ranar Lahadi Sarkin Zazzau marigayi Alhaji Shehu Idris ya rasu bayan da ya kwashe shekara 45 akan karagar mulkin masarautar ta Zazzau.

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG