Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na Biyu Ya Yi Kira ga Fulani su Kare Al'adarsu ta Zaman Lafiya

  • Ibrahim Garba

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na Biyu.

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na Biyu ya yi kira ga Fulani da su rungumi al'adar da'a da zaman lafiya da kakansu Usman Dan Fodio ya gadar masu.

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na Biyu, ya yi kira ga kabilar Fulani da su cigaba da nuna da’a da halaye masu kyau da ya ce sun gada daga kaka da kakanni saboda su zama abin koyi ga sauran mutane. Ya ce ya kamata Fulani su cigaba da jaddada zaman lafiya kamar yadda aka sansu tun asali. Ya yi wannan kiran ne lokacin da Shugabannin kungiyar Miyatti-Allah na kasa baki daya su ka kai masa ziyara.

Wakilinmu na Kano da ya aiko ma na da wannan rahoton, Mahmud Ibrahim Kwari, ya kuma ce a “yayin da mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na Biyu ke kira ga Fulani makiyaya game da zaman lafiya, shi kuwa gwamnan Jigawa Sule Lamido cewa yake tilas ne mahukunta su samar da yanayin kula da hakkin dabbobi ta hanyar samar da filin kiwo da ruwa da kuma burtalai a matsayin matakan magance matsalar baya ga kyautatuwar tattalin arzikin kasa.”

Mahmud Ibrahim Kwari ya ruwaito Mai Martaba Sarkin Kano na cewa, “Kabilar Fulani, tuntuni akwai halaye da dabi’u wadanda su ke alfahari da su, wanda mu na fata dukkan kungiya za a cigaba da tabbatar da ‘ya’yanta akansu, kuma a cigaba da riko da jaddada addini saboda irin aikin da su Shehu Usman Dan Hodio su ka yi bai kamata mu ce mu da mu ka rage daga baya an bar wannan aikin ba. Akwai abubuwa sun a tasowa a kasar nan na fituntunu da fada kullum tsakanin makiyaya da manoma. A yi kokari duk inda ake aga hanyoyin da za a zauna lafiya. ”

Shi kuwa gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya ce daukar matakan kula da hakkokin makiyaya da dabbobinsu ne zai kawo karshen takaddama tsakaninsu da manoma, domin kuwa sun gwada sun gani a jihar Jigawa. Ya ce an ware wurare wajen 50 na shan ruwan dabbobi cike da ciyayi masu kyau ga dabbobi.

Your browser doesn’t support HTML5

RIKICIN MANOMA DA MAKIYAYA