Majalisar Dattawan Najeriya Na Son Bayani Daga Gwamnan Babban Banki Kan Faduwar Darajar Naira

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

Majalisar dattawan Najeriya na son bayani daga gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele kan yadda Naira ke cigaba da faduwa a kusan duk mako kan canjin dalar Amurka.

Majalisar wacce ta gayyaci Emefiele ta bayyana a babban zauren ta, amma kuma kamun nan ta tafi hutun wata biyu.

Dala dai a kasuwar canji ta haura Naira 700 kafin ta dan dawo baya inda a canjin banki ta ke Naira 431.

Tsadar dala da kara farashin litar fetur tuni ya tada farashin muhimman kayan masarufi.

Majalisar ta tattauna kan kin sayarwa kasuwar canji dala da Emefiele ya yi a matsayin hanyar farko da ta karya darajar Naira.

Tsohon shugaban kasuwar canji a Abuja Alhaji Rabi’u Gada ya ce ya zama wajibi ne a hukunta Emefiele matukar za a iya samun wani gyara.

Sanata Sani Musa ya maimata bayanan masana tattalin arziki da ke cewa cikin abubuwan da za su farfado da Naira akwai amfani da kayan da a ke samarwa a cikin gida ta hanyar rage dogaro ga shigo da komai daga ketare.

Nan take masanin tsaro Dr.Yahuza Getso ya ce bai wuce a yi batun noma ba don wadata kasa da abinci da da zai iya taimakawa Naira, amma hakan na da nakasu da tabarbarewar tsaro.

Za a zuba ido a ga ko majalisar za ta ware wani lokaci ne cikin hutun don sauraron Emefiele ko kuwa sai karshen hutun a ranar 20 ga watan satumba.

Saurari cikakken rahoton cikina sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattawan Najeriya Na Son Bayani Daga Gwamnan Babban Banki Emefiele Kan Faduwar Darajar Naira Kan Dala