Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa CBN Ta Dakatar Da Sayar Da Kudaden Waje Ga ‘Yan Canji


Hedkwatar Babban Bankin Najeriya
Hedkwatar Babban Bankin Najeriya

Bankin na CBN ya kuma ce zai dakatar da ayyukan ba da lasisi ga masu neman bude kasuwancin canjin kudaden kasashen waje.

Babban bankin Najeriya CBN, ya ce dalilin da ya sa ya haramta sayar da dala da sauran kudaden kasashen waje ga masu hada-hadar canji a kasar shi ne, ana amfani da su wajen halalta kudaden haram.

Bankin na CBN ya kuma ce zai dakatar da ayyukan ba da lasisi ga masu neman bude kasuwancin canjin kudaden kasashen waje.

“Mun damu, saboda masu ayyukan canjin suna bari ana amfani da su wajen dabbaka ayyukian cin hanci da rashawa.” Gwamnan CBN Godwin Emefiele ya fada yayin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin a ranar Talata.

Ya kara da cewa, “babu yadda za mu ci gaba da zura ido muna kallo ana wannan tabargazar a kasuwannin na canji.”

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

Emefiele ya ce daga yanzu, kudaden kasashen wajen za su rika tafiya kai-tsaye zuwa bankunan kasar.

Rahotanni sun ce tuni har farashin dala yah aura a ranar Talata bayan da babban bankin na Najeriya ya ayyana wannan sabon tsari.

Sai dai ga masanin kimiyar tattalin arziki na kasa da kasa Shu’aibu Idris Mikati, wannan mataki bai dace ba ganin cewa kasuwanci ne da ya ke ba matasa da dama ayyukan yi.

Bankin CBN
Bankin CBN

A cewar shi, in ana da kamfanoni dubu 7 masu daukan ma’aikata 5 to ana samun guraben ayyuka dubu 35 kenan, saboda haka, a tasa fahimtar ba a yi tunani mai zurfi ba.

Mikati ya ba da shawara cewa maimakon hana hada-hadar kudaden, ya fi a kara masu yawan kudin da ake sayar masu da dalar, Misali a tashi daga Naira 410 zuwa 490 sannan su masu canji su dora Naira 5 domin su samu alheri kadan akan kudin, yana mai cewa sokewa gaba daya bai dace ba.

Kudaden dalar Amurka
Kudaden dalar Amurka

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya ce wannan mataki ne da zai karfafa tattalin arzikin kasar ya kuma dakile amfani da masu canji da ke yi wajen halalta kudaden haram.

A shekara 2006 ma an taba daukan irin wannan matakin amma kuma daga baya an soke shi.

Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:

Dalilin Da Ya Sa Muka Dakatar Da Sayar Da Kudaden Waje Ga ‘Yan Canji – CBN
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00


XS
SM
MD
LG