Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Daukaka Kara Kan Dakatar Da Wasu 'Yan Majalisa

Majalisar Dokokin Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce ta daukaka kara zuwa kotun daukaka kara ta Najeriya akan hukuncin babbar kotun tarayya wadda ta haramta dakatarwar da majalisar ta yi wa ‘yayan ta guda biyar a cikin watan Maris da ya gabata, saboda laifin tada tunzuri a zauren majalisar.

Dambarwar mahawara akan wani kudiri da aka gabatar a zauren majalisar wanda ke kunshe da jerin laifukan da aka tuhumi tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, shine lamarin da ya sabbaba dakatar da ‘yan majalisar su biyar.

A yayin mahawarar, guda daga cikin 'yan majalisar ya yi yunkurin fita da sandar girma ta majalisar bisa tallafin ‘yan uwan sa, al’amarin da ya sanya tilas zaman majalisar na wannan rana ya gagara.

Mako guda bayan wannan tarzoma, sai shugabancin majalisar ya sanar da dakatar da wadannan ‘yan majalisa su biyar wadanda suka hada da tsohon shugaban majalisar Isyaku Ali Dan-Ja, da tsohon shugaban masu rinjaye Labaran Abdul.

Sai dai 'yan majalisar sun kalubalanci wannan mataki a gaban kotun tarayya da ke Kano kuma a ranar Laraba 4 ga watan Juni kotun ta ce dakatarwar ta su ba ta bisa ka’ida.

Honourable Salisu Maje Ahmed Gongozo, daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin da kotu ta ce a dawo da su bakin aiki ya ce ko da daidai aka yi ko ba daidai aka yi ba, sun yi biyayya, sun je kotu, kuma yanzu Allah sa sun samu nasara.

To amma shugaban masu rinjaye Honourable Salisu Maje Ahmed Gongozo ya ce majalisa ta zauna ta tattauna kuma kai tsaye ta daukaka kara, yanzu dole kowa ya tsaya a matsayinsa sai lokacin da kotun ta yanke hukunci.

Ya kara da cewa, magana ce ta idan aka kai ka kara in ka yi nasara ko aka yi nasara a kan ka, sai ka auna ka ga abin ya yi ma daidai ko bai ma daidai ba. In ya yi ma daidai ka karba in kuma bai ma daidai ba sai ka daukaka kara domin kana tunanin kotu ta gaba kila ta yi ma abinda ka ke so.

Yanzu hakan dai na nuni da cewa za a ci gaba da fafatawa tsakanin bangarorin biyu a gaban kuliya.

Saurara karin bayani a cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Daukaka Kara Kan Dakatar Da Wasu 'Yan Majalisa