Manjo Al-Mustapha ya Mayarda Martani

Manjo Hamza al-Mustapha

Wasikar da tsohon shugaban Najeriya Obasanjo ya rubutawa shugaban kasar Jonathan ta yi kamar ta shafi Manjo Hamza Al-Mustapha dalili ke nan da ya mayarda martani
Kodayake tsohon shugaban Najeriya Obasanjo bai ambaci sunan Manjo Hamza Al-Mustapha ba a cikin wasikar da ya rubutawa shugaba Jonathan amma masu sharhi kan harkokin siyasar kasar suna zaton akwai inda Obasanjo yake yin hannunka mai sanda dangane da Manjo din.

Yayin da yake magana da manema labarai Manjo Hamza Al-Mustapha ye ce baya nan lokacin da Obasanjo ya rubuta wasikarsa sai dai ya ji labari. Da yana nan ya ce tuntuni da ya mayarda martani. Ya karanta wasikar Obasanjo kuma ya ji abubuwan da mutane suke cewa a kai. Ya ce na farko Obasanjo bai ambaci sunansa ba a wasikar. Na biyu kuma shi Obasanjo ya sanshi. Kuma Obasanjo ya san shi Manjo Hamza ya san Najeriya kamar yadda shi Obasanjo ya san Najeriya. Inda yana da magana da shi Manjo da sai ya yi kai tsaye ya tambayeshi ko kuma ya kalubalanceshi. Ya ce ya kalubali Obasanjo kan duk abun da yake so game da kasar tun ma kafin ya zama shugaba ya tambayeshi koina a duniyar nan zai bada amsa.

Dangane da jita-jitar da a keyi cewa shugaba Jonathan zai yi anfani da Manjo Hamza ya horas da wasu 'yan banga da zasu kashe 'yan hamayya da shi shugaba Jonathan ya rantse babu abu kamar haka. Ya ce shekara da shekaru suka yi suna taimakawa 'yan arewa shiga aikin soji da na 'yansanda da wasu ayyuka masu anfani da kayan sarki kuma shi ba zai yi abun da zai cuci arewa ba. Ya ce shi bai sani ba ko Obasanjo da makarrabansa suna shirya wani abu makamancin hakan. Ya ce shi ya yi hakuri sabili da irin sirin da ya sani da bai ce komi ba.

Dangane da wadanda suka gana masa azaba ya ce wadanda basu da imani suna ganin yafewar ba da gaske ba ne dalili ke nan da suna rabewa suna yin wasu abubuwa. Ya ce a yi addu'a Obasanjo ya yadda su yi mahawara ido da ido a bainar duniya kowa ya jisu domin gaskiya ta fito. Abun da ya sa gaba yanzu shi ne taimakawa kasa da talakawa da matasa da kuma kawo daidaituwa cikin al'umma.

Tun daga shekarar 1974 kawo yanzu akwai abubuwa da yawa da aka rufesu da karerayi kuma yana fata za'a tonosu watarana.

Nasiru Adamu El-Hikaya nada rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Manjo Al-Mustapha Ya Mayarda Martani