Accessibility links

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Karyata Cewa Ta Karawa Al-Mustapha Girma

  • Aliyu Imam

Maj. Hamza Al-Mustapha

A cikin sanarwa da ta bayar rundunar mayakan ta karyata rahotannin cewa ta karawa Manjo Hamza Al-Mustapha girma zuwa mukamin Birgediya Janar.

Rundunar sojojin Najeriya ta sake tabbatar da cewa Manjo Hamza Al-Mustapaha har yanzu yana cikin rundunar sojan Najeriya. Duk da haka rundunar bata bata lokaci ba wajen karyata rade raden cewa ta karawa al-Mustapha girma zuwa mukamin Birgediya Janar.

Wakilinmu Nasiru Adamu El-Hijaya ya hada mana rahoto kan mataki na gaba da watakil Al-Mustapha zai dauka ganin cewa sa'o'insa a soja sun tsere masa.

XS
SM
MD
LG