Martanin Amurka Kan Gwajin Makamin Koriya Ta Arewa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson ya fadi a wata takarda jiya Jumma'a cewa Amurka ba za ta taba yadda Koriya Ta Arewa ta mallaki makamin nukiliya ba. Ya kuma yi kira ga Rasha da China da su dau matakan kawo karshen rashin jituwa a yankuna da ma kasa da kasa wanda shirin makamai masu linzami na Koriya Ta Arewar ke haddasawa.

Takardar bayanin, wadda aka wallafa a shafinsa na Twitter, ta zo ne 'yan sa'o'i bayan da kasar ta yi gwaji na biyu na makami mai linzami na nahiya-zuwa-nahiya, wanda ke iya isa Amurka.

Tillerson ya ce wannan gwajin ya saba ma jerin kudurorin Kwamitin Sulhun MDD, wanda ke bayyana matsayin al'aummar duniya kan wannan batun.

Sojojin Amurka da na Koriya Ta Kudu sun harba makamai masu linzami cikin ruwayen Koriya Ta Kudu, a matsayin wata ramuwar gayya ta kai tsaye saboda gwajin makami mai linzami na nahiya zuwa nahiya da Koriya Ta Arewa ta yi jiya Jumma'a.