Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jeff Sessions Ya Ce Ba Shi Da Niyyar Yin Murabus


Babban lauyan gwamnatin Amurka, Jeff Sessions March 6, 2017.

Kai ruwa rana da ake yi tsakanin shugaba Donald Trump na Amurka da babban lauyan gwamnatin kasar Jeff Sessions na kara ta'azzara yayin da Sessions din ya ce ba shi da niyyar yin murabus.

Babban Atoni Janar din Amurkan Jeff Sessions ya bayyana karara cewar ba shi da niyyar yin murabus daga mukaminsa saboda kakkausar sukar da shugaba Donald Trump ke masa.

Sai dai ya ce zai yi abin da zai kwantar da hankalin shugaban wanda ya ke ta caccakarsa ta a farkon makon nan.

Trump ya ci gaba da nuna matsin lamba a kan Sessions a jiya Laraba.

A wasu sakwannin Twitter guda biyu, Trump ya tambaya cewar mai ya sa Atoni Janar bai kori darektan hukumar bincike ta FBI mai riko Andrew Mc Cabe ba wanda matarsa ta samu makudan kudade na gudunmuwa ga yakin neman zabe daga 'yan jami’iyar Democrat a bara a lokacin da take takara a jihar Virginia.

Trump ya bayyana rashin jin dadinsa ga Sessions a farkon wannan mako, amma ita kuwa mai magana da yawun Fadar White House, Sarah Hucabee Sanders, ta fada a jiya Laraba cewar idan shugaban kasa ya nuna rashin jin dadinsa ga Atoni Janar hakan ba yana nufin ya yi murabus ba ne.

Facebook Forum

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG