Mataimakin shugaban kasar Gambia Badara Alieu Joof ya rasu a India.
Shugaban Adama Barrow ne ya sanar da rasuwar mataimakin nasa a shafin Twitter a ranar Laraba.
“Ina mai alhinin sanar da ku rasuwar mataimakina, mai girma Badara Alieu Joof.” Barrow ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Fellow #Gambians, it is with a heavy heart that I announce the passing away of my #VicePresident, His Excellency, Badara Alieu Joof. The sad event took place in India after a short illness. May Allah grant him Jannahtul Firdawsi.
— President Barrow (@BarrowPresident) January 18, 2023
Ya kara da cewa, “lamarin ya faru ne a India bayan da ya dan yi rashin lafiya. Ina mai fatan Allah ya ba shi gidan Aljanna.”
Shugaba Barrow bai yi karin bayani dangane da rasuwar mataimakin nasa ba.
Asalin Joof malamin makaranta ne da yake koyar da harshen Ingilishi a kwalejin Gambia kafin ya shiga harkar siyasa.