Matasa A Jihar Plato Sun Dauki Matakin Hana Shan Goskolo

Wadansu matasa suna tsalle

Matasan a jihar Plato sun dauki matakin hana shan wani abu mai sa maye da ake kira goskolo da ake hadawa da wadansu miyagun kwayoyin da suka hada da hodar ibilis, wiwi
Matasa a unguwar Rikkos dake karamar hukumar Jos ta Arewa a Jiha Plato sun dauki matakin hana ‘yan’uwansu shan wani abin sa maye da yayi kaurin suna da ake kira Goskolo.

Matasan sun bayyana cewa, sun dauki shawarar yaki da shan Goskolo ne sabili da illarta ga matasa da kuma zaman lafiya a jihar. Bisa ga cewarsu, masu shan irin wannan abin maye suna fita hayacinsu saboda haka yana da sauki a rinjayesu su shiga tada zaune tsaye.

Matasan sun kuma ce wannan abin sa mayen banda talauta al’umma, yana shan jini ya ramar da mashayin wani lokaci har ya kai ga kisa. Kamar yadda wakiliyarmu Zainab Babaji ta ruwaito mana.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasa Sun Dauki Matakin Hana Shan Goskolo - 3:43