Mayakan Ruwan Najeriya Na Nema A Yiwa Dokokin Kasar Gyaran Fuska.

Mayakan Ruwa suna hallartar taron sauyin shugabanci a birnin Abuja Junairu 20, 2014.

Rundunar mayakan ruwan Najeriya ta bada shawarar yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska a fannin harkokin tsaro.

Babban hafsan mayakan ruwan Najeriya, Vice Admiral Ibok Ibas, yace rundunar zata ci gaba da kare diyaucin Najeriya.

Ya bayyana cewa, rundunar mayakan ruwan tana fuskantar kalubalai dake gurguntar da ayyukanta da suka hada da batutuwa irin na diplomasiya, yiwuwar rashin fahinta dake kasashen dake yankin tekun Guinea, da kuma farfaganda da Karin gishiri kan fashin teku da wadansu kafafen yada labarai na kasashen waje ke yi.

Vice Admiral Ibok Ibas ya kuma nemi da a yiwa dokokin kasar nan gyaran fuska, don baiwa sojojin damar, tuhuma da gurfanar da wandada ake zargi da aikata laifuka a cikin ruwa gaban kotu.

Bisa ga cewarshi, rundunar mayakan ruwan Najeriya tayi imanin cewa, idan aka sami kotuna na musamman dake sauraron irin wandannan shari’u, hakan zai karawa mayakan ruwan Najeriya kwarin guiwa.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Hassan Maina Kaina ya aiko daga Abuja, Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoto Kan aikin rundunar mayakan ruwan Najeriya-2"13