Ministan Abuja Ya Kira Taron Gaggawa Sakamakon Yawaitar Sata Da Kashe Mutane

Nyesom Ezenwo Wike

Ministan babban birnin Tarayyar Najeriya, Barrister Nyesome Wike ya jagoranci wani taron tsaro na gaggawa da ya kunshi baki dayan manyan kusoshin tsaron birnin.

ABUJA, NIGERIA - Wannan dai ya biyo ne bayan kara tabarbarewar al'amuran tsaro na satar mutane don neman kudin fansa, inda ministan ya yi ta kokarin kwantar da hankalin mazauna birnin.

A halin yanzu dai gomman mutanen birnin ne ke hannun ‘yan bindiga ana ci gaba da yin garkuwa da su a cikin daji.

Babban abin da ya fi jan hankalin jama'a shine yadda aka sace gomman mutane a baya-bayan nan a yankin karamar hukumar Bwari, inda tuni ‘yan bindigan suka harbe daya daga cikin ‘yan matan da suke tsare da su saboda gaza kai masu kudin fansa na Naira miliyan sittin a cikin lokacin da suka nema.

Daga bisani ‘yan bindigar sun kuma kara hallaka wasu karin mutane biyu tare da kara yawan kudin fansar zuwa Naira miliyan dari bakwai

Hakan kuma ya kara ta da hankalin jama’a, hatta manyan kusoshin gwamnati irin su Dalhatu Ezekiel Musa, kwamishinan hukumar sauraren korafe-korafen jama'a na babban birnin tarayyar.

Ezikiel ya ce ya zama wajibi su fito su yi magana da nufin janyo hankalin shugabanni, ganin wannan matsala ta kai ga hana mutane zuwa gonaki da kuma zama cikin yankunan birnin.

A cewar wani masanin tsaro, Wing Commander Musa Isa Salman, akwai bukatar yin amfani da fasahar zamani wurin tunkarar wannan matsala da sannu a hankali ke kara mamaye baki dayan sassan kasar.

Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:

Your browser doesn’t support HTML5

Ministan Abuja Ya Kira Taron Gaggawa Sakamakon Yawaitar Sata Da Kashe Mutane .mp3