Mutane 16 Sun Rasu A Wani Hari Da Aka Kai Garin Maiduguri

Mutane sun tsere bayan harin kunar bakin waken na, Maiduguri, Najeriya, Talata, Nuwamba 25, 2014.

Wata fashewa da ta auku a wata kasuwa da ake samun cunkoson jama’a yau asabar a arewa maso gabashin Najeriya ya kashe a kalla mutane goma sha shida sama da ishirin kuma suka jikkata.

Wata fashewa da ta auku a wata kasuwa da ake samun cunkoson jama’a yau asabar a arewa maso gabashin Najeriya ya kashe a kalla mutane goma sha shida sama da ishirin kuma suka jikkata.

Bom din ya tarwatse ne da misalin tsakar rana a Maiduguri babban birnin jihar Borno.Rahotanni na nuni da cewa, mai yiwuwa wata karamar yarinya yar shekaru goma ta tada shi.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin harin.

A garin Potiskum kuma, wani jami’in ‘yan sanda ya shaidawa wani dan jarida cewa, bom da ya tarwatse a wata mota da ya kashe mutane biyu, harin kunar bakin wake ne.

Kungiyar mayakan Boko Haram dake tada kayar baya a arewa maso gabashin Najeriya ta sha kai hare hare a Maiduguri da Potiskum.

Wakilinmu Haruna Dauda Bi'u na da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Rahoton harin Maiduguri da Potiskum