Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rahoto Na Musamman Akan Baga: Babi na Biyu


Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima

Sama da shekaru biyar ke nan da Najeriya ke ta alalkakai da kungiyar nan ta 'yan Boko Haram.

Za'a ga bayansu yau ko gobe amma abun sai kara sukurkucewa ya keyi. Kusan a ce wankin hula na neman ya kai kasar zare.

Lamarin ya sa 'yan kasar musamman 'yan arewacin Najeriya basu da kwarin gwiwa ga gwamnati mai ci. A arewacin Najeriya babu wanda ya rage yanzu da kungiyar bata kaiwa hari ba kama daga tsarakuna ko tsoffin jami.an sojoji ko na gwamnati balle mutanen gari.

Yanzu haka dubban mutane ne suka rasa muhallansu sakamakon farmakin da kungiyar Boko Haram ke kaiwa a lokuta daban daban. Lamarin ya bar gwamnatocin arewa suna samar da sansanonin 'yan gudun hijira yayin da wasu sun shige kasashen dake makwaftaka da kasar.

Dubban mutane suka yi asarar 'yanuwansu da dukiyoyinsu masu dombin yawa. Wani ma da yayi gudun hijira daga Baga ya taka zuwa Maiduguri tafiyar wajen kilomita dari biyu. Yace kodayake an kawowa sojoji kayan aiki amma duk da haka sai da suka gudu suka barsu 'yan Boko Haram su hallakasu.

To saidai lamarin Boko Haram ya zame alkaikai ga ma duniya baki daya. Idan an dubi irin hare-haren da kungiyar ta sha kaiwa a lokuta daban daban ya isa hujja domin hatta ginin Majalisar Dinkin Duniya dake babban birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja, bai sha da dadi ba. A ranar 27 ga watan Agustan 2011 kungiyar ta kai masa hari kuma mutane da yawa suka mutu sakamakon harin.

A lokuta daban daban kungiyar ta kame wasu 'yan kasashen waje ta kuma hallakasu. Haka kuma ta kai hari a babban ofishin 'yansanda dake Abuja. Wannan ya nuna cewa babu wani wuri da yafi kafrin kungiyar ta kai hari domin har barikokin sojoji ta kai hari sau tari.

Babu wani wuri da kungiyar ba zata iya kai hari ba saidai idan an sake lale kamar yadda Tukur Abdulkadir masanin harkokin yau da kullum ya shaida. Yace ba laifi ba ne idan kasashe masu tasowa sun hada kai musamman wadanda suke kusa da juna da kuma suke da al'ada iri daya. Amma bai kamata a ce manyan kasashe suna tsoma baki cikin alamuransu ba. Hakan baya haifar ma kasashen da mai ido.

Yadda kungiyar Boko Haram ta samu horaswa akan sarafa makamai abun dubawa ne. Yanzu haka tana da makamai wadatattu kuma wadanda suka fi na jami'an sojojin Najeriya inganci.

Ko bayan shigo da makamai da kungiyar tayi haka kuma ta kware wajen sarafa bam tare da tadashi wanda har yanzu sai kara ta'azara ya keyi. To amma Dr Bawa Abdullahi Wase masani akan harkokin tsaro yace muddin gwamnatin tarayya ba sake salo tayi ba to haka kullum kungiyar Boko Haram zata cigaba da samun galaba ne. Yace kamata yayi gwamnati ta sani cewa barin wasu su shigo da makamai da nufin tursasawa wani bangaren kasar tamkar mafarki ne domin ba zai yi tasiri ba. Haka kuma yin muamalada miyagun mutane cikin gwamnati ba zai haifi da mai ido ba. Dole gwamnati tayi aiki da kwararru kuma masu kishin kasa.

Shi ma gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, jihar da ta fi kowace shan ukubar Boko Haram,yace duk yake-yaken duniya daga karshe sai an kaiga yin sulhu.Kodayake shi yana son a yi sulhu amma karfinsa bai kai ba. Gwamnati tarayya ke da wannan karfin. Sai dai ya bada shawara.

Akan zaben da za'a yi wata mai zuwa Sanata Ma'aji Lawal dan garin Baga yace batun zabe ma bai taso ba tukun. Babu yadda za'a yiwa mutane maganar zabe cikin irin halin da suke ciki saidai wanda bashi da hankali. Amma hukumar zabe tace babu inda ba za'a yi zabe ba a duk fadin tarayyar kasar.

Ga cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:30 0:00

XS
SM
MD
LG