Mutane Na Cigaba Da Tofa Albarkacin Bakinsu Sanadiyar Hare-hare A Nijar

Dubban 'yan Nijar su na zanga-zanga a Niamey, babban birnin kasar

Sanadiyar hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan garuruwan Agadez da Arlit da suke da cikakken matakan tsaro masana na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu.
Sanadiyar hare-haren kunar bakin wake da aka kai kan garuruwan Agadez da Arlit da suke da cikakken matakan tsaro masana na cigaba da bayyana ra’ayoyinsu.

A nasu ra’ayin an kai hare-haren ne da nufin tsorata da kuma razana mutane domin yan tsageran su ci karensu ba babbaka.

Sun ce lamarin tamkar an yaudari kasar Nejar ne domin an tsare iyakoki domin kada ire-iren wadannan mayakan su shigo.

Ba’a yi la’akari da wadanda suke cikin kasar a wurare daban-daban ba.

Kungiyoyin fararen hula na ganin lokaci ya yi da Nijer zata sake salon tsaro. A nasu ra’ayin kada Nijer ta daga murya tana son ta yi yaki da irin wadannan yan tsageran.

A harin da aka kai sama da mutane ashirin suka rigamu gidan gaskre da yan kunar bakin wake biyu.

Abdullahi Maman Ahmadu na da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutane a Nijar sun ci gaba da tofa albarkacin bakinsu