Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bindige Wasu Maharan Nijar Su Biyu


Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou da yake ganawa da manema labarai a Afrika ta Kudu. Nov. 11, 2011.

Sojojin Faransa da Nijar sun bindige wasu karin masu tsattsauran ra’ayin Islama biyu, da ke cikin wadanda su ka kai hari kan wani barikin soji da ke arewacin Nijar.

Wani dan jaridar da ke wajen ya gaya wa Muryar Amurka cewa dakarun musamman na Faransa ne su ka jagoranci farmakin na yau Jumma’a da aka kai don karya lagwan ‘yan bindigar, wadanda su ka makale a barikin, bayan harin kunar bakin waken da harbe-harben da aka kai jiya Alhamis.

Ministan Tsaron Nijar ya tabbatar da kashe mutanen da hannun dakarun Faransa a farmakin. Akwai rahotonnin da ke cin karo da juna game da halin da mutanen da ‘yan bindigar su ka yi garkuwa da su.

‘Yan bindiga masu tsattsauran ra’ayin Islama sun kai hari kan barikin a garin Agadez da kuma kamfanin hakar ma’adanin Uraniyum mallakin Faransa a Arlit a lokaci guda jiya Alhamis da safe. Harin da aka kai barikin sojojin ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 20, wadanda akasarinsu sojojin Nijar ne.

Kungiyar tsattsauran ra’ayin Islama ta MUJAO da ke Mali ta dau alhakin kai harin, kamar yadda shi ma tsohon shugaban kungiyar al’kaida shiyyar arewacin Afirka Mokhtar Belmoktar shi ma ya yi ikirari.

Sun ce harin martani ne ga jagorancin da kasar ta Faransa ke yi a yakin da ake yi da mayaka masu tsattsauran ra’ayin Islama a Mali.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG