Najeriya: An Bukaci Gwamnatoci Su Kara Kasafin Fannin Ilimi

Yayin da masana a fagen harkokin ilimi a Najeriya ke nanata muhimmancin gudunmawar al’uma wajen farfado da bangaren ilimi na kasar, gwamnatin jihar Kano ta ce shirin ta na ilimi kyauta kuma dole ya kunshi inganta tsarin makaratun tsangayu.

Shirin ya kaikaci bangaren koyar da fannonin ilimi na addinin Musulinci, tare da darrusan ilimin zamani a lokaci guda.

A shekarar da muka yi ban kwana da ita ne gwamnatin ta Kano ta kaddamar da dokar ta-ba-ci a bangaren ilimi na jihar, inda ta kirkiro abin da ta kira tsarin Ilimi kyauta, kuma dole daga makarantun Firamare zuwa Sakandare.

Shirin dai ya kunshi kula da sha’anin koyo, da koyawar a makarantun tsangayu, inda za’a rinka koyar da darrusan zamani kamar lissafi da turanci ga daliban ko almajiran makarantun.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da masana a fagen ilimi a Najeriya ke jaddada muhimancin gundunmawar al’umma wajen farfado da sha’anin ilimi a kasar.

Bayan gudunmawar al’umma a matakan ilimi daban-daban, masu kula da al'amura a fannin ilimi na Najeriya na ganin akwai bukatar gwamnatoci su kara adadin kudaden da suke kebewa ilimi a kasafinsu na shekara-shekara.

Ga cikakken rahoto cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Najeriya: An Bukaci Gwamnatoci Su Kara Kasafin Fannin Ilimi