Najeriya ta Samu Nasara Kan Yaki da Polio

Ma'aikatan Polio

Anyiwa fiye da yara dari biyu da suka kamu da cutar polio fida

Najeriya ta samu gagarumin nasara kan yaki da cutar shan inna inji Ministan kiwon lafiya Dr. Haliru Alhassan.

Yace kawo yanzu jihohin Kano da Yobe ne kadai ake da wadanda suka kamu da cutar a bana kuma mutane hudu ne kawai a duk fadin Najeriya.

Yace a bara an yiwa fiye da yara dari biyu aiki fida da kuma taimakamasu da takalma da zai taimakamasu wajen tafiya,hakan ya samu ne da hadin kan wasu kwararru daga ksasashen waje.

Ya furta haka ne a wata hira da suka yi da wakilin mu Aliyu Mustapha a birnin Washington DC.

Yace wannan nasaran ba zai rasa nasaba da ingancin da aka samu ba wajen yakin da ake da cutar ta shan inna ta hanyoyin riga kafi.

Ministan,ya kara da cewa Sarakuna da shuwagabanin addini suma sun taka rawar gani a yakin da ake yin da cutar ta shan inna.

Your browser doesn’t support HTML5

Nasara Akan Polio a Najeriya - 4'21"