Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hari Kan Filin Jirgin Sama


Filin jirgin saman Entebbe.

Harin Ta'addanci kan filin jirgin sama a kasar Uganda.

Ofishin jakadancin Amurka dake Uganda yayi gargardi game da yiwuwar wani harin ta'addanci a kan babban filin jirgin saman Entebbe a kasar Uganda.

Ofishin ya fada a shafinsa na Intanet cewa majiyoyin leken asiri sun ce akwai wata "takamammiyar barazanar" da aka samu daga wata kungiyar ta'addanci cewa zata kai hari kan filin jirgin saman yau alhamis 3 Yuli tsakanin karfe 9 zuwa karfe 11 na dare.

Ofishin yace ya samu bayanin wannan barazana ce daga rundunar 'yan sandan Uganda.

Ofishin ya bukaci matafiya da zasu bi ta wannan filin jirgi da su sake nazarin shirinsu, su kuma yi hattara.

XS
SM
MD
LG