NAJERIYA: Tsohon Shugaban Hukumar Kwastan Abdullahi Dikko Inde Ya Rasu

Abdullahi Dikko Inde.

Rahotanni daga babban birnin Tarayya Abuja na nuni da cewa, tsohon shugaban hukumar Kwastan na Najeriya Dikko Inde ya rasu a babban birnin tarayya Abuja bayan doguwar jinya

Abdullahi Dikko Inde wanda ya rike mukamin shugaban hukumar kwantan tsakanin shekara ta 2009 zuwa 2015, ya rasu yana da shekaru 61 a duniya.

An haifi Abdullahi Dikko ranar 11 ga watan Mayu a garin Musawa da ke jihar Katsina. Ya kuma kamala makarantar sakandare a shekara ta 1974 zuwa 1980 a kwalejin gwamnati ta Kaduna.

Tsohon shugaban hukumar Kwastan Abdullahi Dikko Inde

Ya yi karatun digiri na farko da na biyu a fannin ilimin kimiyya a jami’ar Dimitrov Apostle Tshenov, da Svishtov, a kasar Bulgaria.

Ya kama yi aiki a hukumar kwastan a shekarar 1988 inda ya rike mukamai daban daban da suka hada da shugabancin rundunonin hukumar a kan iyakar Seme, da jihar Imo da Badagry. Ya kuma zama babban jami’i mai gudanar da bincike kafin zaben shi shugaban hukumar a shekara ta 2009, mukamin da ya rike na tsawon shekaru shida.

Za a yi jana’izar shi gobe a babban Masallacin tarayya da ke Abuja bayan sallar jumma’a.

shugaban-hukumar-kwastan-ya-yi-ritaya

kano-daidaituwa-tsakanin-hukumar-kwastan-da-yan-kasuwa

hukumar-shiga-da-fice-ta-kama-kayan-biliyoyin-nairori

Karin bayani akan: Abdullahi Dikko Inde, Hukumar Kwastan, Nigeria, da Najeriya.