NIJER: Takun Saka Tsakanin Masu Mulki Da Jam’iyyar Lumana Kan Bacewar Wasu Makudan Kudade

Hayaniyar data taso bayan bayyanar labarin miliyan dubu dari biyu na kudin Sefa (CFA) da ake zargin wasu mukarraban gwamnati da karkatarwa da kuma wasu muhimman abubuwanda a ‘yan kwanakinnan sun sa ‘yan Nijer matsawa hukumomi lamba domin karin haske a kansu.

Wannan lamari na daya daga cikin batutuwan da jam’iyyar PNDS-Tarayya ta ce jam’iyya mai adawa, wato MORDEM-Lumana, na amfani da su ne kawai domin ta ruda ‘yan kasar.

Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin daya daga cikin jigon jam’iyyar PNDS-Tarayya, Alhaji Kalla Muntari, a wata sanarwa da yayi, inda ya ce “maganganu marasa kyau da ‘yan siyasa ke so su maida tamkar al’ada a wannan kasar sune maganganun da suka shafi kabilanci da tsaron kasa” saboda an tono wadannan kudi CFA Miliyan dar biyu da ba a san yadda aka yi da su ba”

Da yake mayar da martani, shugana ruko na jam’iyyar MORDEM-Lumana, ya danganta zarge zargen na PNDS-Tarayya a matsayin masu nasaba da siyasa.

Jam’iyya mai mulki ta ja kunnen magoya bayan jam’iyyar MORDEM-Lumana, cewar idan masu ruruta maganganu makamantan wadannan basu bari ba, to lallai fa kwai hukuncin da doka ta tanada akan irinsu, dan haka idan kunne ya ji to gangar jiki ya tsira.

Domin Karin bayani ga rahoton da Sule Mumuni Barma, daga jamhuriyar Nijer ya aiko mana.

Your browser doesn’t support HTML5

NIJER: Takun Saka Tsakanin Masu Mulki Da Jam’iyyar Lumana Kan Bacewar Wasu Makudan Kudade