Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Nijar Ta Amince da Kafa Dokar Ta Baci a Jihar Tawa


Majalisar Dokokin Nijar
Majalisar Dokokin Nijar

Yawaitar hare-haren 'yan ta'adda a wasu wurare cikin jihar Tawa ya tilastawa Majalisar Dokokin kasar Nijar amincewa da kafa dokar ta baci a wasu gudumomin jihar

Yawaitar hare-haren 'yan ta'adda a wasu wurare cikin jihar Tawa ya tilastawa Majalisar Dokokin kasar Nijar amincewa da kafa dokar ta baci a wasu gudumomin jihar.

Harin ta'addancin da jihar ke fama da shi ya samo asali ne daga kasar Mali wadda take makwaftaka da kasar Nijar a bangaren jihar ta Tawa.

Wannan shi ne karon farko da majalisar dokokin Nijar ta amince da kafa dokar ta baci a jihar. Dokar ta shafi gundumomi kaman irinsu Tiliye da Tasara.

Gwamnan jihar Musa Abdulrahaman ya jagoranci taron majalisar tsaro ta jihar tare da halartar shugabannin gungumomin da dokar ta shafa tare da shugabannin tsaron jihar.

Dokar ta hana zirgazirgan ababen hawa daga karfe takwas na yamma zuwa karfe shida da rabi na safe idan ba tare da izinin shugabannin gundumomin ba. An ba jami'an tsaro izinin bincike koina dare da rana. Haka kuma duk wanda yake da bindiga an umurceshi ya je wurin jami'an tsaro ya mika masu.

Inji gwamnan jihar sun rufe wasu kasuwanni dake kan iyakar kasar da Mali ta bangaren jihar saboda sun kasance masu hadarin gaske. Kasuwannin sun zama mafakar masu sayar da kwaya da makamai. Gwamnan yace tayin hakan ne zasu kawowa jihar cikakken kwanciyar hankali.

Ga karin bayani daga rahoton Haruna Mamman Bako.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:36 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG