Ra’yoyin Wasu ‘Yan Jihar Borno Game Da Sakin ‘Yan Matan Chibok 82

Shugaba Muhammadu Buhari Da 'Yan Mata 82 Da 'Yan Boko Haram Suka Sako

Biyo bayan nasarar da gwamnati Najeriya ta samu na cimma yarjejeniya da kungiyar Boko Haram, inda aka sako wasu daga cikin ‘yan matan Chibok har su 82 shugabannin da mutanen jihar Borno sun tofa albarkacin bakinsu.

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya yi bayani ga al’ummar jiharsa da kuma mika godiyarsa ga shugaba Mohammadu Buhari da kuma rundunar sojan kasar game da nasarar da suka samu na sake ‘yanto ‘yan matan Chibok.

Da suke bayyana ra’yoyinsu wasu mazauna garin Maiduguri, kan sakin ‘yan matan Chibok da aka yi shine rashin samun cikakken bayani game da ‘yan kungiyar Boko Haram din da aka yi musayarsu da ‘yan matan 82.

Abin tambaya dai anan shine manene makomar mayakan Boko Haram din da aka saka? Shin zasu koma su dauki kayan yaki su ci gaba da kashe al’umma ko kum sun tuba? Yanzu dai abin da al’umma ke jira su gani shine cikakken bayanan irin yadda aka kubutar da ‘yan mata da kuma irin halin da suke ciki.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda Biu.

Your browser doesn’t support HTML5

Ra’yoyin Wasu ‘Yan Jihar Borno Game Da Sakin ‘Yan Matan Chibok 82 - 3'36"