Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Matan Chibok Da Aka Sako Sun Sauka A Abuja


'Yan matan Chibok a Abuja

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace yana da yakinin cewa suma sauran 'yan matan za a sako su

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa an sako ‘yan mata tamanin da biyu cikin fiye da su dari biyu da ‘yan kungiyar Boko haram suka sace.

Kakakin shiugaban Najeriya, Garba Shehu, ya bayan cewa an sako ‘yan matan ne baya da aka cimma yarjejeniyar sako wasu daga cikin ‘yan kungiyar dake hannun gwamnati.

Malam Garba Shehu ya ce shugaba Muhammadu Buhari, na da karfin guiwar cewa suma sauran ‘yan matan da suka rage za a samu karbo su, ya kuma yi godiya ga dakarun tsaron Najeriya, gwamnatin kasar Switzerland, kungiyar Red Cross da kungiyoyi masu zaman kansu a ciki da wajen Najeriya.

Dama sako ‘yan matan Chibok na daya daga cikin alkawuran da shugaba Buhari yayi a lokacin yakin neman zaben da yah au dashi mulkin Najeriya.

Tuni dai wadannan ‘yan mata suka sauka a birninm Abuja domin saduwa da shugaba Muhammadu Buhari.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG