Rikicin Gabashin Kasar Ukraine Ya Hallaka Mutane Bakwai

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko

Kasar Ukraine ta ce mutane a kalla 7 sun mutu a wani fadan da aka shafe kwanaki biyu ana gwabzawa tsakanin 'yan tawaye masu ra'ayin Rasha da sojojin gwamnati a gabashin Ukraine da yaki ya daidaita.

Bangarorin biyu na zargin juna da tayar da tashin hankalin baya-bayan nan, wanda gwamnati ta ce ranar Lahadi aka fara a wurare da dama da ke yankin gabashin kasar mai amfani da harshen Rasha, ciki har da tungar Donetsk da ke karkashin ikon Rasha da kuma wani yankin da ke kusa da kan iyakar Rasha.

Ukraine na zargin 'yan tawayen da takalo tashe-tashen hankulan, ta wajen amfani da tankokin yaki da gurnet-gurnet. Irin wadannan manyan makaman na cikin jerin wadandan aka haramta bisa ga yarjajjeniyar da aka cimma a 2015, wadda ta yi matukar taimakawa wajen rage barna da kashe-kashe a yankin da ake takaddama akai.

A Donetsk, jagororin 'yan tawaye da ke gwagwarmayar neman 'yancin cin gashin kai daga Ukraine sun ba da rahoton lalata abubuwa da dama masu nasaba da farar hula, su ka kuma ce sun katse ruwa da wutar lantarki na kauyuka da dama.