Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Kasashen Duniya Su Tunkari Tsokanar Fada da Rasha Keyi -Joe Biden


Mataimakin Shugaban Amurka Joe Bidenda shugaban Ukraine Petro Poroshenko jiya a Kiev

Ahalinda ake ciki kuma, mataimakin shugaban Amurka Joe Biden yace tilas ne hukumomin kasa da kasa su tunkari tsokanar fadan da Rasha ta keyi. Daga nan yayi kira ga shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump, ya baiwa Ukraine cikakken goyon baya da zama babban kawarta.

Da yake magana jiya Litinin a Kiev babban Birnin Ukraine a gefen shugaban kasar Petro Poroshenko, Biden ya lura cewa Ukraine tana "yaki da cin hanci da rashawa da ya zama mata sankara, da kuma takalar fada daga fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin."

Kalaman Trump, lokacin da yayi hira ta hadin gwuiwa da jaridun Times of London da Bild ta Jamus, inda ya nuna cewa yana tunanin cimma yarjejeniya da Rasha da zai kawo karshen takunkumin da aka kakabawa kasar, idan ta amince kasshen biyu su rage yawan makaman Nukiliya da suke da su.

Biden yace tilas a ci gaba da amfani da takunkumin da aka azawa Rasha bayan da ta kama ta kuma hade zirin Crimea da Rasha a shekara ta 2014.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG